The Insider(22): "SIYASAR MANZO (S.A.W) A MAHANGAR SIRA (I)"By
Salim I. Hassan
21/05/2017

“Hakika Manzo ya zo muku yana karanta muku sakon Allah (Wahayi) a bayyane, domin ya fitar da wadanda su ka yi imani suka aikata ayyukan na gari daga duhun (halaka) zuwa ga Hasken (tsira)”. (Sura 65- At-talaq aya 11).
Haka Allah (S.W.T) ya fassara manzo (s.a.w) a cikin al-Qur’ani mai girma. Amma sakon cikin ayar bawai kawai ya isuwa ga wadanda suka rayu a zamaninsa ba ne a’a ana Magana da har wadanda zasu zo a lokacin gaba. A saboda haka ne Annabi (s.a.w) ya zama manzon karshe. Babu wani manzo da zaizo bayansa, babu wani wahayi da zai kara sauka. Illa iyaka wadanda sukai imani das hi zasu iya amfani da sirarsa a kowane lokace, a kowane ne wuri domin fitar da kansu daga abin day a shige musu duhu na daga mas’alar rayuwa.

Wane Duhun halaka ne manzo ya zo ya fitar damu daga ciki? Shi ne duhun kafirci irin na quraishawa, da kin gaskiya irin na yahudawa da nasaran wancan zamanin.
A yau kuma kololuwar duhun kafirci a zamanin mu shine wanda turawan yammacin duniya ke wakilta ta hanyar yada fahimtar wayewarsu a rayuwa a hannu daya; da kum yadda kasashen musulman duniya suka fada wani yanayi na bijirewa tsarin Allah a rayuwarsu ta duniya a daya hannun. Wannan halin da duniya ke ciki a yau shine kwatancin zamanin jahiliyyar baya wadda manzo (s.a.w.) ya sha fama wajen kawar da ita. Amma jahiliyar yau ta fi zama gama gari saboda westan sibilaizeshan ya game kowan bangare da yanaki na  duniya. Babu shakka al’umar yau ta kara nutsewa cikin zurfin duhun jahiliyya a dai-daikun mu da tarayyarmu. Kalma daya da zata fassara yanayin da muka tsinci kanmu ayau shine muce: Al’umarmu ta komawa jahiliya ba tare da ta fita daga cikin musulunci ba. A haka ne muma sai muka tsinci kanmu a cikin irin matsalar da ta fuskanci babban madubin rayuwa (s.a.w). Sai ta bayyana cewa hanyar da zata fitar damu kawai shine mubi hanyar da  yabi. Saboda haka dole mu sabunta duban tsanaki ga Sirarsa da kuma Sunnar sa (s.a.w) domin samun mafita a yau.

To amma ya za’ayi abi sirarsa ba abu ne mai sauki ba ayau saboda ba zamu iya amfani da ita a irin yadda aka rubuta ta a litattafan tarihi. Sira da Sunna kamar al’Qur’ani suke, suma kundin ilimi ne da ake iya neman shiriya da su a kowane zamani. Sirar manzo (s.a.w) tana nan domin bincike, sake rubutata da fahimtarta da yin amfani da ita a duk wani abin tarihi da ke faruwa na daga zamantakewarmu, dangantakarmu da sauran al’uma, yake-yake, zaman sulhu, da sauransu. Abin fahimta anan shine watakila kowacce  sabuwar al’umma zata iya amfani da Sira a matsayin sabon madubin zamatakewar siyasarta a duk wani al’amari day a shafi irin zamaninta. Illa iyaka dole abi tsarin ‘Da koyo akan Iyawa’ kafin mu iya riskar ainihin koyarwar sira a yanayin da muke ciki a yau.

Dalilin da yasa nace ba zamu iya amfani da Sira a irin yadda aka rubutata a litattafan tarihi ba shine malaman da suka rubutata a lokacinsu sun banzatar da bangaren karfin ikon musulunci a siyasance, suka maida hankali kawai kan rubutun mutuntakar manzo (s.a.w) da siffofinsa. Al-waqidi, Ibn Ishaq da Ibn Hisham duk sunyi kokari sosai wajen bin saukakkiyar hanyar tattara bayanai da lissafin abubuwan da suka faru a tarihance a litattafan sirarsu.  Babu wani kokari daya bayyana karara wajen danganta al’amura daga wannan zuwa wancan, ko kuma kokarin fito da gwagwarmayar diflomasiya da dabarun siyasa da Manzo (s.a.w) yayi amfani da su wajen cimma nasara.  Daga cikin irin wadanna muhimman abubuwa da akai watsi dasu a wajen rubuta sirar sa (s.a.w) akwai ‘Power’ (Karfin Iko), samar da ita a lokacin da babu ita, amfani da ita a sanda aka sameta, da kuma sarrafata ta hanyar da ta dace domin cimma manufar da aka sa a gaba.

MENENE ‘POWER’ (KARFIN IKO)?
Power a musulunce iri biyu ce: akwai boyayyiyar (Spritual) power da kuma bayyananniyar (Physical) power. Boyayyiyar power itace karfin iko na imanin da muka yi da Allah da Manzon sa (s.a.w). Wannan power bata bukatar wata ma’aikata ko kungiya ko sojoji domin wanzar da ita. Mazaunin wannan power itace zuciyar mutum. Babu wani karfin soji da zai iya kawar da wannan power. Adalcin shugaba, gaskiyarsa, kyautatawarsa da kuma iya kalamansa shi ke samar da wannan power a zuciyoyin mabiyansa.

Idan muka duba Sira za mu ga cewa tsawon shekaru 13 da Manzo (s.a.w) yayi a Makka yana da’awa wannan power ya dasa a zukatan tsirarun mutanen da suka amsa kiran Allah. Sai ya zamana basu da wani karfin yawa ko na makami ko na dukiya ko na mulki amma dogaransu da karfin imanin da suka kwankwada daga Manzo (s.a.w) amma Quraishawa sun rasa ya za suyi da tsirarin musulmai a Makka tare da cewa su ked a karfin mulki, kudi da makamai amma duk a banza. Musulmai basu samu Physical power ba har sai bayan Hijra a Madina.
YA MATSAYIN POWER TA KE A YAU, KUMA YA MASU ITA SUKE GUDANAR DA ITA A DUNIYAR YAU…… SIYASAR MANZO (S.A.W) A MAHANGAR SIRA KASHI NA (II)
ZAMU CI GABA A JUMA’A MAI ZUWA IN SHA ALLAH

No comments:

Post a Comment

THE INSIDER

TRUMP: THE MOST CONFUSED ONE.....

The confused man can no longer be at ease.