By
Salim I. Hassan
21/05/2017
“Hakika Manzo ya zo muku yana karanta muku sakon Allah (Wahayi) a
bayyane, domin ya fitar da wadanda su ka yi imani suka aikata ayyukan na gari
daga duhun (halaka) zuwa ga Hasken (tsira)”. (Sura 65- At-talaq aya 11).
Haka Allah (S.W.T) ya fassara manzo (s.a.w) a cikin al-Qur’ani mai
girma. Amma sakon cikin ayar bawai kawai ya isuwa ga wadanda suka rayu a
zamaninsa ba ne a’a ana Magana da har wadanda zasu zo a lokacin gaba. A saboda
haka ne Annabi (s.a.w) ya zama manzon karshe. Babu wani manzo da zaizo bayansa,
babu wani wahayi da zai kara sauka. Illa iyaka wadanda sukai imani das hi zasu
iya amfani da sirarsa a kowane lokace, a kowane ne wuri domin fitar da kansu
daga abin day a shige musu duhu na daga mas’alar rayuwa.
Wane Duhun halaka ne manzo ya zo ya fitar damu daga ciki? Shi ne
duhun kafirci irin na quraishawa, da kin gaskiya irin na yahudawa da nasaran
wancan zamanin.
A yau kuma kololuwar duhun kafirci a zamanin mu shine wanda turawan
yammacin duniya ke wakilta ta hanyar yada fahimtar wayewarsu a rayuwa a hannu
daya; da kum yadda kasashen musulman duniya suka fada wani yanayi na bijirewa
tsarin Allah a rayuwarsu ta duniya a daya hannun. Wannan halin da duniya ke
ciki a yau shine kwatancin zamanin jahiliyyar baya wadda manzo (s.a.w.) ya sha
fama wajen kawar da ita. Amma jahiliyar yau ta fi zama gama gari saboda westan
sibilaizeshan ya game kowan bangare da yanaki na duniya. Babu shakka al’umar yau ta kara
nutsewa cikin zurfin duhun jahiliyya a dai-daikun mu da tarayyarmu. Kalma daya
da zata fassara yanayin da muka tsinci kanmu ayau shine muce: Al’umarmu ta
komawa jahiliya ba tare da ta fita daga cikin musulunci ba. A haka ne muma sai
muka tsinci kanmu a cikin irin matsalar da ta fuskanci babban madubin rayuwa
(s.a.w). Sai ta bayyana cewa hanyar da zata fitar damu kawai shine mubi hanyar
da yabi. Saboda haka dole mu sabunta
duban tsanaki ga Sirarsa da kuma Sunnar sa (s.a.w) domin samun mafita a yau.
To amma ya za’ayi abi sirarsa ba abu ne mai sauki ba ayau saboda
ba zamu iya amfani da ita a irin yadda aka rubuta ta a litattafan tarihi. Sira
da Sunna kamar al’Qur’ani suke, suma kundin ilimi ne da ake iya neman shiriya
da su a kowane zamani. Sirar manzo (s.a.w) tana nan domin bincike, sake
rubutata da fahimtarta da yin amfani da ita a duk wani abin tarihi da ke faruwa
na daga zamantakewarmu, dangantakarmu da sauran al’uma, yake-yake, zaman sulhu,
da sauransu. Abin fahimta anan shine watakila kowacce sabuwar al’umma zata iya amfani da Sira a
matsayin sabon madubin zamatakewar siyasarta a duk wani al’amari day a shafi
irin zamaninta. Illa iyaka dole abi tsarin ‘Da koyo akan Iyawa’ kafin mu iya
riskar ainihin koyarwar sira a yanayin da muke ciki a yau.
Dalilin da yasa nace ba zamu iya amfani da Sira a irin yadda aka
rubutata a litattafan tarihi ba shine malaman da suka rubutata a lokacinsu sun
banzatar da bangaren karfin ikon musulunci a siyasance, suka maida hankali
kawai kan rubutun mutuntakar manzo (s.a.w) da siffofinsa. Al-waqidi, Ibn Ishaq
da Ibn Hisham duk sunyi kokari sosai wajen bin saukakkiyar hanyar tattara
bayanai da lissafin abubuwan da suka faru a tarihance a litattafan sirarsu. Babu wani kokari daya bayyana karara wajen
danganta al’amura daga wannan zuwa wancan, ko kuma kokarin fito da gwagwarmayar
diflomasiya da dabarun siyasa da Manzo (s.a.w) yayi amfani da su wajen cimma
nasara. Daga cikin irin wadanna muhimman
abubuwa da akai watsi dasu a wajen rubuta sirar sa (s.a.w) akwai ‘Power’ (Karfin
Iko), samar da ita a lokacin da babu ita, amfani da ita a sanda aka sameta, da
kuma sarrafata ta hanyar da ta dace domin cimma manufar da aka sa a gaba.
MENENE ‘POWER’ (KARFIN IKO)?
Power a musulunce iri biyu ce: akwai boyayyiyar (Spritual) power da
kuma bayyananniyar (Physical) power. Boyayyiyar power itace karfin iko na
imanin da muka yi da Allah da Manzon sa (s.a.w). Wannan power bata bukatar wata
ma’aikata ko kungiya ko sojoji domin wanzar da ita. Mazaunin wannan power itace
zuciyar mutum. Babu wani karfin soji da zai iya kawar da wannan power. Adalcin
shugaba, gaskiyarsa, kyautatawarsa da kuma iya kalamansa shi ke samar da wannan
power a zuciyoyin mabiyansa.
Idan muka duba Sira za mu ga cewa tsawon shekaru 13 da Manzo
(s.a.w) yayi a Makka yana da’awa wannan power ya dasa a zukatan tsirarun
mutanen da suka amsa kiran Allah. Sai ya zamana basu da wani karfin yawa ko na
makami ko na dukiya ko na mulki amma dogaransu da karfin imanin da suka
kwankwada daga Manzo (s.a.w) amma Quraishawa sun rasa ya za suyi da tsirarin
musulmai a Makka tare da cewa su ked a karfin mulki, kudi da makamai amma duk a
banza. Musulmai basu samu Physical power ba har sai bayan Hijra a Madina.
YA MATSAYIN POWER TA KE A YAU, KUMA YA MASU ITA SUKE GUDANAR DA
ITA A DUNIYAR YAU…… SIYASAR MANZO (S.A.W) A MAHANGAR SIRA KASHI NA (II)
ZAMU CI GABA A JUMA’A MAI ZUWA IN SHA ALLAH